Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jam'iyyar PDP, Mohammed Abacha ya nemi babbar kotun Tarayya a Kano ta tilastawa hukumar zaɓe ta INEC tabbatar ma sa da takararsa

 Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jam'iyyar PDP, Mohammed Abacha ya nemi babbar kotun Tarayya a Kano ta tilastawa hukumar zaɓe ta INEC tabbatar ma sa da takararsa.

Abacha ya kalubalanci hukuncin da ya tabbatar da cewa Sadiq Wali ne sahihin ɗan takarar PDP a Kano.


Mohammed Abacha ya ce shi ne ya lashe zaben fitar da gwamni da aka gudanar a ranar 25 ga watan Mayu wanda ya ce INEC ta tura wakilai domin sa ido, amma sai kuma aka musanya sunansa da Sadiq Wali.

Mai neman takarar na son kotu ta hana PDP da shugaban jam'iyyar na Kano gabatar da Wali a babban zaben da ke tafe a 2021.

Akwai dai rarabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP da ke da tsagi biyu a Kano.

Wannan dalilin ne ya sa bangarorin da ke rikici da juna kowa ya gabatar da na shi zaben fitar da gwanin.

Abin da ya kai ga PDP ta samu 'yan takara biyu kafin daga bisani aka tabbatar wa da Sadiq Wali kujerar takara.

Sai dai Mohammed Abacha tun daga wannan lokaci ya ke kalubalantar matsayar jam'iyyar da maka batun a gaban kotu.

A cikin watan Satumba za a cigaba da sauraron karar.

Post a Comment

Previous Post Next Post